Philippians 2

1Idan akwai wani abin karfafawa cikin Almasihu. Idan da wata ta’aziyya daga kaunarsa. Idan akwai zumunta a Ruhu. Idan da tatausan jinkai da tausayi. 2Ku cika farin cikina don ku zama da tunani irin haka, kuna da kauna daya, kuna tarayya cikin Ruhu daya, ku kasance da manufa iri daya.

3Kada ku yi komai cikin sonkai ko girman kai. A maimakon haka cikin zuciya mai tawali’u kowa na duban wadansu fiye da kansa. 4Kada kowa ya dubi bukatun sa, amma yana lura da bukatun wadansu.

5Ku yi tunani cikin hanya wadda ke cikin Almasihu Yesu. 6Wanda ya yi zama cikin siffar Allah, bai mai da daidaitarsa da Allah wani abin da zai rike ba. 7Maimakon haka, ya wofintar da kansa. Ya dauki siffar bawa. Ya bayyana cikin kamannin mutane. An same shi a bayyane kamar mutum. 8Ya kaskantar da kansa, ya yi biyayya har ga mutuwa, mutuwa ta gicciye.

9Saboda haka Allah ya ba shi mafificiyar daukaka. Ya ba shi suna wanda yafi kowanne suna. 10Domin a cikin sunan Yesu kowace gwiwa za ta durkusa, gwiwoyin wadanda ke cikin sama da kuma duniya da kuma karkashin duniya. 11Kuma kowanne harshe zai furta cewa Yesu Almasihu Ubangiji ne, zuwa daukakar Allah Uba.

12Domin wannan kaunatattuna, kamar yadda kullum kuke biyayya ba sai ina nan kadai ba. Balle yanzu da bananan, ku yi aikin cetonku da tsoro da far gaba. 13Gama Allah ne yake aiki a cikinku ku yi nufi duka da aikata abin da zai gamshe shi.

14Ku yi kowanne abu ba tare da gunaguni da gardama ba. 15Domin ku zama marasa abin zargi kuma masu gaskiya, ‘ya’yan Allah marasa aibi. Ku yi haka domin ku haskaka kamar haske a cikin wannan duniya, a tsakiyar karkatacciyar da gurbatacciyar tsara. 16Ku rike kalmar rai da karfi domin in sami dalilin daukaka Almasihu a ranarsa. Sa’annan zan san cewa ban yi tseren banza ba, ban kuma yi wahalar banza ba.

17Ko da ana tsiyaye ni kamar sadaka a kan hadaya da kuma hidimar bangaskiyarku, na yi farin ciki, kuma na yi farin ciki tare da ku duka. 18Kamar haka kuma sai ku yi farin ciki, ku yi farin ciki tare da ni.

19Amma na yi niyya in aiko da Timoti wurin ku ba da dadewa ba, domin ni ma in sami karfafuwa idan na san al’amuran ku. 20Gama bani da wani wanda halinmu yayi daidai da nasa, wanda yake juyayin ku da gaskiya. 21Domin duka ribar kansu suke nema bata Yesu Almasihu ba.

22Amma kun san darajar sa, kamar yadda da ke hidimar mahaifisa, haka ya bauta mani cikin bishara. 23Shi nake sa zuciyar in aiko maku ba da dadewa ba idan naga yadda al’amura nake gudana. 24Amma ina da gabagadi cikin Ubangiji cewa ni da kaina zan zo ba da dadewa ba.

25Amma ina tunanin yakamata in sake aiko maku da Abafaroditus, shi dan’uwana ne, abokin aiki, da abokin yaki, manzon ku da kuma bawa domin bukatu na. 26Da shike yana marmarin ku duka, ya damu kwarai da shike kun ji yayi rashin lafiya. 27Da gaske yayi rashin lafiya har ya kusan mutuwa. Amma Allah ya ji tausayin sa, ba shi kadai ba, amma har da ni, domin kada in yi bakin ciki kan bakin ciki.

28Domin haka na yi niyyar aiko shi, saboda idan kun sake ganinsa za ku yi farin ciki ni kuma in kubuta daga juyayi. 29Ku karbi Abafaroditus da dukan murna cikin Ubangiji. Ku ga darajar mutane irin sa. Domin saboda aikin Almasihu ne ya kusan mutuwa. Ya sadakar da ransa domin ya bauta mani domin ya cika hidimar da ya kamata ku yi mani.

30

Copyright information for HauULB